Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

GHANA:Kungiyar Amnesty Ta Yi Allah Wadai Da Kisan Farar Hula


Kungiyar Amnesty International Ghana
Kungiyar Amnesty International Ghana

Kungiyar Amnesty International mai fafutukan kare hakkokin bil adama ta bayyana damuwa game da wasu matakan da jamian tsaron kasar Ghana suka dauka akan fararen hula tare da ‘yan jarida, abinda yayi sanadiyar rasa rayuka tare da jikkatar wasu.

KUMASI, GHANA - Kungiyar na jawabi ne yayin da take gabatar da rahoton ta na shekara shekara, inda ta bukaci gwamnati ta dau matakai domin ganin ta kare hakkokin ‘yan kasa.

A bara ne wasu dakarun soja suka bude wuta akan wasu al’ummar Zangon Ejura dake Jihar Ashanti yayin da al’ummar ke zanga zangar nuna damuwarsu bisa kazamin kisan da aka yi ma wani saurayi Muhammad Kaaka da aka ce mamban kungiyar matsin lamba ta FIXTHECOUNTRY ne.

Mutane biyu ne suka rasa rayukansu kazalika wasu suka jikkata sakamakon matakin da dakarun suka dauka. Mallam Usama Armiyau , mai tattaro matasan kungiyar matsin lamba ta Economic Fighters League yayi maraba da kiran da Amnesty International tayi ma gwamnati.

Kodinatan raya ci gaban zango tare da tsakiyar birane kana lauya mai kare hakkokin bil Adama Honorable Ben Abdallah Banda ya ce gwamnati ta baiwa iyalan wadanda suka rasa rayukan su sakamakon harin da sojoji suka kaima fararen hulan zangon Ejura diyya tare da tantance wadanda suka jikkata domin samar masu diyya da ta dace.

To sai dai ba anfani da karfi fiye da kima akan fararen hula kadai ne kungiyar ta yi Allah wadai akai ba, har da cinkoson fursunoni a gidajen yari, abinda mataimakin shugaban babban gidan yarin Kumasi.

Kungiyar Amnesty International ta kuma ce cin zarafin mata ya karu kazalika hare hare akan masu luwadi da madigo ya tsananta tun lokacin da aka gabatar da kudirin haramcin luwadi da madigu a majalisar dattawa da tilastawa mutane ficewa matsugunansu ya sanya jama'a da dama cikin mawuyacin hali a kasar.

Saurari rahoto cikin sauti daga Hamza Adam Kumasi Ghana:

Kungiyar Amnesty International Ta Yi Allah Wadai Da Matakan Jami’an Tsaron Ghana Suka Dauka Da Yayi Sanadiyar Kiasan Farar Hula
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00

XS
SM
MD
LG