ACCRA, GHANA - Kiraye kirayen na zuwa ne a dai dai lokacin da ministan tsaron kasar Albert Kan Dapaah ya sanar da wasu matakan da gwamnati ke dauka domin tabbatar da tsaron ciki da wajen kasar, biyo bayan rikicin kabilanci da na filaye da fashi da makamai da dai sauransu ke barazana ga tsaron kasar.
Mallam Irabad Ibrahim mai sharhi bisa harkar tsaron ciki da wajen kasar Ghana na ganin muddan ba'a baiwa matasa dama ba to shakka ba bu za 'a iya cimma manufar karfafa tsaron kasar ba sabida batun tsaro ya shafi kowane dan kasa inji shi.
Sai dai kuwa shugaban kungiyar masu sanya idanu a matsugunan Ghana Mallam Faisal Ismael ya ce mafi yawanci mambobin kungiyar tsaron 'yan sa kai da ake kira "National Neighborhood Watch Committee" matasa ne, kuma suna sanya idanu bisa shige da ficen al’umma da dama, don haka akwai muhimmanci sosai da gwamnati ta maida hankali akan matasa.
Alhaji Sibawai Papa Angola daya daga cikin masu ruwa da tsaki bisa harkokin matasan Ghana kana makusanci ga Limamin kasar ya bukaci gwamnati ta ringa sauraran masu ruwa da tsaki cikin harkar matasa musamman masu kokarin sulhunta tsakanin matasa aduk lokacin da aka samu barkewar rikici.
Ya bada misali da rikicin musulmi da krista a birnin Kumasi da rikicin musulmi da krista a Hohoe na Jihar Volta da kuma rikicin baya bayanan nan tsakanin wasu matasa a Nima dake Accra a inda yake cewa matasa sun bada gudunmuwa sosai gurin sulhunta tsakanin bangarori biyun, a don haka kamata ya yi da gwamnati ta maida hankali akan matasa sosai, inji shi.
Kasar Ghana dai ta tsinci kanta tsakiyar kasashen da aka kai hare-hare masu nasaba da ta'addanci abinda wasu masana ke ganin ka iya zamowa babban barazana ga yanayin tsaron kasar.
Saurari rahoto cikin sauti daga Hamza Adams: