Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ghana Da Wasu Kasashen Afirka Shida Sun Fara Cinikayya Karkashin Yarjejeniyar AfCFTA


 Ghana Da Wasu Kasashen Afirka Shida Sun Fara Cinikayya A Karkashin AfCFTA
Ghana Da Wasu Kasashen Afirka Shida Sun Fara Cinikayya A Karkashin AfCFTA

Ghana da wasu kasashe shida sun fara cinikin kayayyaki da ayyuka, kwanaki kadan bayan an samu dace kan mataki na farko na tsarin yadda kasuwancin zai kasance, a karkashin shirin gudanar da cinikayya tsakanin kasashen Afirka marasa shinge (AfCFTA)

ACCRA, GHANA - Kodinetan AfCFTA na kasa, Dokta Fareed Arthur ne ya bayyana hakan a Accra, wajen kaddamar da taron karawa juna sani na makarantar sabuwar shekara da jami’ar Ghana ke shiryawa karo na 74.

Ghana Da Wasu Kasashen Afirka Shida Sun Fara Cinikayya A Karkashin AfCFTA
Ghana Da Wasu Kasashen Afirka Shida Sun Fara Cinikayya A Karkashin AfCFTA

Kasashen sun hada da Kamaru, Masar, Kenya, Rwanda, Tanzania, da Mauritius. Ghana dai ta aika da man ja, da kashu (cashew) zuwa Kenya da Kamaru, yayin da Kenya ta aika da gahwa (coffee), ganyen shayi, da batiran mota zuwa Ghana.

Yayin da yake jawabin kaddamar da taron ‘karawa juna sani da jami’ar Ghana ke shiryawa duk shekara, wanda aka yi wa taken, ‘Saisaita Kasuwar Afirka domin tabbatar da ci gaban tattalin arziki mai dorewa ta hanyar AfCFTA’ Dokta Fareed Arthur ya kara da cewa,"Kafa AfCFTA a shekarar 2018 na daya daga cikin mafi kyawun lamarin ci gaba da ya fito daga Afirka tun lokacin da aka kafa kungiyar Tarayyar Afirka”.

Masana na nuni da cewa wannan cinikayyar da suka fara a tsakaninsu zai taimaka musu da ‘yan kasuwansu bai daya.

Ghana Da Wasu Kasashen Afirka Shida Sun Fara Cinikayya A Karkashin AfCFTA
Ghana Da Wasu Kasashen Afirka Shida Sun Fara Cinikayya A Karkashin AfCFTA

Nuhu Eliasu, malamin ilmin harkokin kudi da tattalin arziki a jami’ar Islama dake Ghana ya ce, tsadar kaya zai yi sauki; za a samu kasuwanci ya bunkasa, gwamnati za ta samu kudaden shiga da za ta yi wa jama’a aiki, a karshe kudaden da za a samu sanadiyar cinikayyar duka za su tsaya nan Afirka maimakon su fita zuwa wasu nahiyoyin.

Shi ma masanin tattalin arziki, Hamza Adam Attijjany ya tofa albarkacin bakinsa a kan yadda wannan cinikayya ta AfCFTA za ta taimakawa kasashen Afirka baki daya ta samun kasuwa mai girma ba tare da shinge ba, yadda ‘yan kasuwa za su shiga kasashen juna domin cinikayya; kuma AfCFTA ta tabbatar da cewa za a sarrafa kayayyaki yadda za a samu farashi mai kyau, wanda zai taimakawa ‘yan kasuwa da gwamnatoci baki daya.

Ana sa ran a shekarar 2023, adadin kayayyakin zai ninka sau uku yayin da kasashen ke karuwa. Kuma manazarta sun yi imanin cewa cinikayya tsakanin yankuna na iya tashi zuwa akalla kashi 33% a cikin shekaru goma masu zuwa tare da fadada kasuwancin mutane biliyan 1.2.

Saurari cikakken rahoto daga Idris Abdullah Bako:

 Ghana Da Wasu Kasashen Afirka Shida Sun Fara Cinikayya A Karkashin AfCFTA.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:38 0:00

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG