A bisa tanadin dokar man fetur ministar tace hakinta ne ta sanar da samun rage farashin litar mai da nera goma, wato daga nera casa'in da bakwai zuwa tamanin da bakwai.
Rage farashin ya soma ne daga daren jiya Lahadi.Dama can gwamnatin Jonathan ce ta kara kudin man daga nera 65 zuwa 97. Ministar tace ta umurci hukumar dake kula da farashin man fetur da ta tabbatar an bi sabon farashin sau da kafa domin anfanin duk 'yan Najeriya.
Ragewar ba zai rasa nasaba da faduwar farashen gangar mai a kasuwar duniya ba inda ya fadi daga dala 65 zuwa 45.
Shugaban kwamitin sufuri na majalisar wakilai Musa Sarkin Adar yace ragin har yanzu bai wadatar ba. Farashen kasuwar duniya ya fadi da kashi hamsin sabili da haka kamata yayi gwamnati ta rage farashinta da kashi hamsin ba nera goma ba kawai. Bai kamata farashin ya wuce nera 45 kowace lita.
Ga rahotoon Nasiru Adamu El-Hikaya.