Burin Atletico Madrid na lashe kofin gasar La Liga a bana, ya gamu da cikas, bayan da Athletic Bilbao ta lallasa ta da ci 2-1.
Hakan wata dama ce da Barcelona ta samu na darewa saman teburin gasar a makon nan.
Har yanzu dai Atletico ce a saman teburin da maki 73.
Amma Barcelona da ke matsayi na uku a teburin da maki 71 bayan da ta doke Villareal da ci 2-1 a ranar Lahadi, za ta iya hawa saman darewa sama idan ta doke Granada a ranar Alhamis mai zuwa.
A kusan karshen wasan, ‘yan wasan Diego Simone (Atletico) sun yi kukan kura suka yunkuro, amma aka karya musu lago, bayan da dan wasan Athletic Inigo Martaninez ya zura kwallo ta biyu a minti na 86.
Wannan kaye da Atletico ta sha, ya kara dagula al’amura, inda maki uku ya raba ta da Sevilla da ke matsayi na hudu – Sevilla ta doke Granada da da ci 2-1, tana kuma da sauran wasa biyar.
Real Madrid da ke rike da kofin gasar, na matsayi na biyu da maki 71 bayan da ta tashi canjaras a gida da Real Betis a ranar Asabar.
Wasa na gaba da Atletico za ta buga shi ne da Elche da ke taga-taga a gasar, gabanin ta tunkari babban wasa mai cike da kalubale da Barcelona a ranar 8 ga watan Mayu.