Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gasar AFCON: “Kun Nuna Jajircewa Matuka”, Tinubu Ya Jinjinawa Tawagar Super Eagles

Shugaban Kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yabawa irin kwazon da Tawagar Super Eagles ta nuna a wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar afrika (AFCON) data gudana a kasar Ivory Coast.

Duk da rashin nasarar da suka yi a hannun masu masaukin baki, Tinubu yace Super Eagles ta nuna kwarewa da jajircewa a gasar.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hadimin shugaban kasar akan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale, ya fitar a lahadin data gabata.

Ivory Coast ce tayi nasara a wasan karshe na gasar afcon ta 2023 bayan data doke takwararta ta super eagles da ci 2 da 1.

Tinubu ya kara da cewar tawagar Najeriyar ta samu gagarumar nasara a idanun al’ummar nahiyar Afrika dama duniya baki daya.

A cewar sanarwar, Shugaba Bola Tinubu ya yabawa tawagar Super Eagles saboda irin kwazon da suka nuna a wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar Afrika data gudana a kasar Ivory Coast.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG