Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya shigar da mawallafin jaridar Daily Nigerian, Ja’afar Ja’afar kara, inda ya nemi kotun ta sa ya biya shi Naira biliyan 3 saboda a cewar shi, ya bata mai suna.
Ja’afar, mawallafin jaridar wacce ke fitowa a yanar gizo, ya fitar da wasu hotunan bidiyo a kwanakin baya, wadanda suka nuna gwamna Ganduje yana karbar rashawar miliyoyi daloli daga hannun ‘yan kwangila.
Jaridar yanar gizo ta Premium Times wacce ta ruwaito cewa ta ga takardar shigar da karar, ta wallafa cewa lauyan gwamna Ganduje, Nuruddeen Ayagi, na neman Ja’afar ya bayyana a gaban kotu nan da kwanaki 14.
Lauyan gwamnan har ila yau, ya nemi kotu ta dakatar da Ja’afar daga wallafa wasu karin hotunan bidiyo a nan gaba ta kowacce irin kafa.
Sai dai a lokacin da Muryar Amurka ta tuntubi ja’afar, ya ce har yanzu ba a ba su kwatankwaciyar takardar karar da aka shigar akan su ba.
A watan da ya gabata, Majalisar Dokoki jihar ta Kano ta kafa kwamiti domin ya binciki wannan lamari, inda ya gayyaci Ja’afar ya bayyana a gabansa.
Ja'afar ya kuma je ya gabatar da bahasinsa a gaban kwamitin.
Sai dai da kwamitin ya gayyaci gwamna Ganduje, sai ya tura kwaminishinan yada labaransa Muhammad Garba.
A dai farkon makon nan, wata kotu ta ba majalisar dokokin jihar umurnin ta dakatar da wannan binciken da take yi.
Facebook Forum