Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gamayyar Kungiyoyin Farar Hula Ta Najeriya Ta Dorawa Hukumomi Alhakin Rashin Tsaro


Masu garkuwa da mutane
Masu garkuwa da mutane

Gamayyar kungiyoyin fararen hula sama da 40 sun kai karar Shugaban Najeriya Bola Tinubu, inda suka yi kira gare shi da ya magance matsalar rashin tsaro da ta kara kamari tun bayan hawansa mulki a watan Mayun da ya gabata.

Koken ya biyo bayan wasu sace-sacen da aka yi a babban birnin tarayya Abuja da kuma jihar Ekiti da ke kudu maso yammacin kasar.

A wani rahoto da gamayyar kungiyoyin farar hula suka fitar a wannan makon, an bayyana cewa, an kashe akalla mutane 2,400 tare da yin garkuwa da wasu kusan 1,900 tun watan Mayun bara lokacin da Tinubu ya karbi mulki.

Kungiyar ta ce ta damu matuka da tabarbarewar tsaro a fadin Najeriya inda ta yi kira ga hukumomi da su dauki matakan da suka dace don magance matsalar.

Auwal Rafsanjani, babban daraktan cibiyar kare hakkin fararen hula, wanda ya yi magana a madadin kungiyar yace, “Rashin tsaro ya mamaye kasarmu, ‘yan ta’adda sun mamaye kasarmu, ‘yan fashi da makami, ‘yan bangar siyasa, ana kashe ‘yan Najeriya kamar tururuwa, Kowace ranar da kuka farka, sai dai a ji kisa bayan kisa, ba za mu iya ci gaba da zama a haka ba."

Auwal Musa Rafsanjani
Auwal Musa Rafsanjani

Rahoton ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da kai munanan hare-hare a kasar ciki har da Abuja.

A birnin Abuja, wasu gungun masu dauke da makamai sun kai hare-hare na garkuwa da mutane domin neman kudin fansa a makonnin da suka gabata. An kashe mutane biyu daga iyalai daban-daban a matsayin gargadi ga wadanda ba su biya ba.

A jihar Ekiti da ke kudu maso yammacin kasar, a kwanakin baya wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da daliban makaranta shida da malamai uku. Hari ila yau, a ranar, wasu ‘yan bindiga suka kuma kai hari a wasu kauyukan jihar tare da kashe wasu sarakunan gargajiya guda biyu.

Tinubu ya yi Allah-wadai da hare-haren sannan ya umarci jami’an tsaro da su kamo wadanda suka kai harin.

Sai dai wani mai sharhi kan harkokin tsaro Chidi Omeje ya ce gazawar gwamnati ce ta haifar da matsalar da ake fama da ita.

Tushen duk wadannan abubuwa shine rashin shugabanci, rashin shugabanci ke haifar da talauci, takaici, da fushin jama'a, in ji shi. "Duba, akwai alaka tsakanin talauci, rashin shugabanci da kuma yaduwar aikata laifuka."

A bara, Tinubu ya sha alwashin magance matsalolin tsaro a Najeriya idan har aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.

Bayan hawansa mulki, Tinubu ya yi wa wasu hafsoshi ritaya tare da nada sabbi.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG