Masu shirya gangamin nan da ake kira "You Stink" sun bayyana shafin Facebook cewa zanga-zangar da suka shirya yi yau litinin da maraice a birnin Beirut ba zai yiwu ba, kuma zasu sake nazarin bukatunsu.
An Soke Zanga-Zangar Da Aka Yi Niyyar Yi Yau Litinin A Lebanon

1
Ma'aikatan kwashe shara su na kokarin tsabtace titi kusa da ginin gwamnati, kwana guda bayan mummunar zanga-zangar da aka yi kan rashin kwashe shara a Beirut, Lebanon, Litinin 24 Agusta 2015.

2
Ministan harkokin cikin gidan Lebanon, Nohad Machnouk, yana ziyarar tsakiyar birnin Beirut kwana guda a bayan mummunar zanga-zanga kan rashin kwashe shara

3
'Yan sandan kwantar da tarzoma na Lebanon su na fesa ruwa domin kokarin tarwatsa masu zanga-zanga kan rashin kwashe shara a tsakiyar birnin Beirut, lahadi 23 Agusta 2015.

4
'Yan sandan kwantar da tarzoma na Lebanon su na fesa ruwa domin kokarin tarwatsa masu zanga-zanga kan rashin kwashe shara a tsakiyar birnin Beirut, lahadi 23 Agusta 2015.