Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firayim Ministar Birtania Ta Yaba Da Matakin Da Amurka Ta Dauka Kan Rasha


 Theresa May, Firayim Ministar Birtaniya
Theresa May, Firayim Ministar Birtaniya

Amurka ta kori 'yan diflomasiyar Rasha 60 daga kasarta a matsayin martani akan zargin da ake yiwa Rasha na kai hari kan Birtania da makamai masu guba da duniya ta haramta

Prime Ministan Birtaniya Theresa May ta yaba da "Martani mai karfi Amurka ta dauka" na korar jami'an diflomasiyyar Rasha su 60, bayan da aka aza laifin cewa hukumomin kasar dake Moscow sune suke da alhakin kai hari da sinadarai masu guba kan tsohon dan leken asiri Rasha dake zaune Birtaniya.

Sanarwan data fito daga fadar gwamnati kasar ta Birtaniya da ake kira Downing Street,tace May tayi Magana da shugaba Trump ta wayar tarho, tana shaida masa cewa Birtaniya ta ji dadin matakin da Amurka ta dauka cutar da Serkei Skripal da diyar sa a garin Salisbury a Birtaniya a farkon wannan watan.

Yanzu haka kasashe sama da 20 ne suka bi sahun Amurka na korar jamian diflomasiyyar kasar ta Rasha a kasashen su.

Sai dai Rasha tayi kemadagas ta karyata wannan zargi.

Amma kuma duk da haka sai da minmistan harkokin wajen kasar ta Rasha Sergey Lavrov, yace ba tantama Rasha zata mayar da martini nan da sati guda kan wannan mataki da Amurka ta jagoranta.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG