WASHINGTON, D.C - Rundunar sojan Koriya ta Arewa ta barazanar cewa zata dauki matakan da bata fayyace ba idan hukumomin Koriya ta Kudu basu nemi gafara ba akan zanga-zangar da mutanensu suka yi jiya Litinin, inda har suka kona wasu gumakan shugabannin Koriya ta Arewa din.
Sanarwar da hukumomin na Koriya ta Arewa suka bada a cuikin kafofinsu na watsa labarai sun yi anfani da irin lafuzzan da suka saba masu zafi, kamar cewa zasu yi anfani da “hammer mai kaifi” wajen yin ramuwar gayya akan abinda suka kira “wannan mummunan hali abin kyama” da masu zanga-zangar suka nuna.
A nan Washington, shugaba Barack Obama yace yana sa ran za’a ci gaba da ganin irin wannan hali na tsokana da neman tada-zaune tsaye a wajen shugabannin na Koriya ta Arewa.