Fillon, wanda ya ce ai ya biya matarsa ne kudin da ya cancanci irin aikin da ta yi. Amma ya roki gafara domin abin da ya kira, "kuskure" saboda daukar iyalinsa aiki. Sai dai ya hakikance albashin da ya ba matarsa ya dace sosai ganin cewa masaniya ce a fannin shari'a.
"Babu wanda ke da damar yin alkalanci kan irin aikin da ya kamata hadimar Majalisar Dokoki ta yi, sai shi kansa dan Majalisar," a cewar Fellon a wani taron manema labaran da ya kira jiya Litini, a martanin da ya bayar game da zargin cewa matarsa bata yi aikin komai ba, duk kuwa da an yi ta biyanta albashin dala $4,000 a wata.
Farin jinin Fillon ya zube matuka a cikin makonni biyu da su ka gabata, tun bayan da jaridar Canard Enchaine ta wallafa wani rahoto mai kunshe da bayanin albashin matar ta Fillon.