Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

FILATO: INEC Ta Cire PDP A Jerin Jami'iyyun Da Zasu Shiga Zabe


Ofishin hukamar INEC
Ofishin hukamar INEC

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta cire jami'iyyar PDP a jerin jami'iyyun da zasu shiga zaben da zata gudanar na 'yan majalisun tarayya a shiyyar Arewacin jahar Filato. 

Gudanar da zaben ya biyo bayan shara'ar da kotun daukaka kara ta yanke, inda ta cire sanata mai wakiltar Filato ta Arewa, Simon Mwadkon da dan majalisa mai wakiltar Bassa da Jos ta Arewa, a Majalisar wakilai, Musa Agah, bisa hujjan cewa jami'iyyar PDP bata da shugabanni kafin gudanar da zaben na 2023.

Mataimakin kakakin jami'iyyar PDP a jahar Filato, Alhaji Abdullahi Garba Mai Rake yace tun suna jin kashin-kishin har dai ya tabbata ba sunan jami'iyyar su a cikin zaben na ranar Asabar.

Shugaban kungiyar gamayyan jami'iyyu ta IPAC a jahar Filato, Abubakar Dogara yace basu da hurumin canza matakin da hukumar zaben ta dauka, sai dai jama’a su yi hakuri su gudanar da zaben cikin lumana.

Mai fashin baki kan lamura kuma shugaban kungiya mai zaman kanta ta CLEEN, Gad Shamaki Peter yace kotu ce kadai zata kwace wa PDP 'yancin ta.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa tace zaben na yau Asabar zai cike guraben sanatoci uku, da wakilan Majalisar tarayya goma sha bakwai, da 'yan majalisun dokoki jaha guda ishirin da takwas a kananan hukumomi tamanin a jihohi ishirin da shida na Najeriya.

Saurari cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG