Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA na duba yiwuwar maye gurbin mataimakan alkalan wasa da fasahar na’urar mutum-mutumi da ake kira robots.
Mataimakan alkalan wasan kwallon kafa sun kusa zama tarihi, ya yin da hukumar FIFA ta samar da wata tawaga da zata binciki yadda yin amfani da fasahar zamani a fagen kwallon kafa.
Samar da fasahar mataimakan alkalan wasa da aka kira Video Assistance Referee ko VAR a takaice da hukumar FIFA ke shirin yi, fasaha ce da aka fara amfani da ita a wasannin wannan kaka ta Firimiya.
Duk da yake cewa fasahar VAR ta haifar da kace-nace kan amfani da ita a wasannin kwallon kafa, sai dai fasahar ta tabbatar da cewa ita ce hanya mafi inganci wajen ganowa idan ‘yan wasa suka shiga offside lokacin wasa.
Yanzu haka dai an yi imanin masu wannan bincike suna duba yadda wannan fasaha za ta shafi wasanni a fadin duniya, a kokarin gano cewa zata inganta wasannin ko sabanin hakan.
A bangaren shiga offside, na’urar daukar hoto ta gano wasu abubuwa masu yawa wadanda badan haka ba babu wanda zai san abin da ya faru, kan haka ne ake ganin FIFA na son amfani da fasahar mutum-mutumi wajen inganta wasanni.
Facebook Forum