Babu haufi ko kadan kan irin mummunan tasirin da da tashe tashen hankalin da ‘yan bindigan Naija Delta kan yi kan tattalin arzikin Najeriya. Bisa alakari da yadda hakan ke shafar adadin danyen mai da kasar ke hakowa a rana.
Ziyarar da wakilinmu Lamido Abubakar ya kai inda ake hakar danyen man ya tabbatar da irin asarar da ake yi samakon fasa bututun mai da matasa zauna gari banza da kuma ‘yan bindiga ke yi. Banda haka kuma ana fama da tashe tashen hankula da tada kayar baya da wadansu mazauna yankunan musamman matasa ke yi, inda suke neman kamfanonin man su dauki kwararan matakan inganta rayuwar mazauna yankunan.
Shirin ahuwar da aka yiwa mazauna yankunan Naija Delta da kuma shigar da su da aka yi cikin harkokin tsaro ya sa sace sace mutane, musamman turara, suka lafa, said ai alkaluma sun nuna cewa, satar danyen mai da kuma fasa bututun mai basu lafa ba.
Wadansu da wakilinmu ya yi hira da su, sun yi korafin cewa, al’umarsu na mutuwa sabili da yunwa yayinda yaransu kuma basu zuwa makaranta. Ta bayyana cewa, suna matukar fama da talauci da wahala a yankin sakamakon lalata muhalli da kamfanonin mai suka yi.
Ga cikakken rahoton da wakilinmu a Patakwal Lamido Abubakar ya hada.