An bayyana kiran da tsohon Hafsan sojojin Nijeriya Janar T.Y. Danjuma ya yi, na a kama shugabannin tsagerun Naija-Delta irinsu Asari Dakubo da Tompolo da sauran masu barazanar tayar da yaki muddun gwaninsu bai yi nasara ba a zaben Nijeriya na ranar Asabar 14 ga watan Fabrairu, da cewa magana ce da ta dace sosai, musamman ganin irin halin da ake ciki a Nijeriya.
A hirarsu da abokiyar aikinmu Maryam Dauda, wani mai sharhi kan al’amuran yau da kullum kuma shugaban kungiyar matasa masu sa ido kan zabe, mai suna Aminu Aliyu, ya ce ba yau masu wannan barazanar su ka fara ba. Ya ce sun sha yin irin wadannan kalamai masu tayar da hankali a lokuta da dama a baya ba tare da an ja masu kunne ba. Ya ce ko a baya ma, wasu ‘yan Nijeriya sun nuna damuwarsu game da irin wadannan kalaman amma babu abin da aka yi. Ya ce barazanar baya bayan nan da Dokubo Asari ya yi cewa matukar Shugaba Goodluck Jonathan ya fadi a zaben Shugaban kasa to ‘yan tsagerun Naija-Delta za su kaddamar da yaki na tabbatar da cewa babu abin da ya cancanci Dokubo a halin yanzu kamar kamu, saboda ya yi nisa baya jin duk wani kira na ya daina tayar da fitina.
Malam Aliyu ya ce Janar Danjuma babban mutum ne a Nijeriya kuma dattijo, don haka ya kamata ‘yan Nijeriya, musamman ma hukumomin da abin ya shafa, su dauki maganar Janar Danjuma da muhimmanci. Ya ce matukar hukuma ba ta dau wani mataki kamar yadda Janar Danjuma ya ba da shawarar a yi ba, to hakan ya nuna Kenan Shugaban kasa ya kasa sauke nauyin da ya rataya a wuyansa na tsare rayuka da dukiyar kasa sannan kuma hakan ya nuna Shugaban Kasar na goyon bayan abin da ‘yan tada kayar bayan ke barazanar yi.