Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fari Na Barazana Ga Jama'ar Somaliya


Wani mutum ya na kallon yadda wani ran rakumi ya salwanta saboda matsalar fari
Wani mutum ya na kallon yadda wani ran rakumi ya salwanta saboda matsalar fari

Shugaban Somaliya Mohammed Abdullai Farmajo ya ayyana kasar a matsayin wacce ta shiga halin ni-‘yasu, yayin da kasar ta shiga matsanancin bala’in matsalar rashin ruwa da kuma karancin abinci.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce wannan kalubalen da Somaliya ke fuskanta na yin barazana ga mutane 6.2 miliyan, adadin da ya kai sama da kashi 50 hamsin cikin dari na mutanen kasar.

Yanayin karancin ruwan ya fi kamari ne a arewacin kasar.

Fitar da amfanin gona ya shafu sosai da kuma raguwar adadin dabbobi bayan da aka fuskanci karancin ruwan sama cikin shekaru biyu a jere.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce farin da ake fama da shi ya na kuma taimakawa wajen yada cututtuka.

Majalisar Dinkin Duniya kuma ta ce tun daga farkon watan Janairu, mutane sama da dubu shida ne suka kamu da cutar amai da gudawa kana wasu 2,500 suka kamu da cutar kyanda.

Yanzu haka dai Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da wata gidauniyar tallafi ta neman Dala miliyon 825, tallafin da za a yi amfani da shi a watannin shida na farko na shekarar nan ta 2017.

A shekarar 2011 Somaliya ta yi fama da matsalar yunwa wacce ta halaka kimanin mutane dubu 2060.

Somaliya na daga cikin kasashen gabashin Afrika da suke fama da matsanancin fari da rashin abinci, tare da Sudan ta Kudu, da Kenya, da Tanzania da kuma Mozambique.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG