Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fara Karbar Haraji Daga Masu Buga Wayar Salula A Najeriya


Wayar Salula
Wayar Salula

Gwamnan babban bankin Najeriya ya baiwa gwamnati shawarar duba yiwuwar fara karbar haraji daga masu buga wayar salula da ya haura mintuna uku, domin samun kudin shiga.

Godwin Emiefele, gwamnan babban bankin Najeriya yace idan aka samu nasarar kaddamar da hakan kasar zata samu kudin shiga kimanin Naira Biliyan Dubu 100 a shekara. Sai dai yace wannan mataki ba zai shafi masu karamin karfi ba, domin kuwa za a rika cajar harajin ne daga wadanda suka buga wayar da ta haura minti uku kacal, wanda kuma yace dawuya a samu talakan dake buga waya sama da mintuna uku.

Wakilin sashen Hausa na Muryar Amurka ya zanta da wasu ‘yan Najeriya a jihar Lagos, yayin da wasu ke ganin yin hakan ba zai takura ba, wasu kuwa na ganin wannan wata hanyar zalunci ce ga talaka domin akwai hanyoyi masu yawa da yakamata gwamnati ta mayar da hankali akai maimakon ta kiran waya.

A cewar gwamnan dai, gwamnati zata iya samun Naira Biliyan 100 a karshen kowacce shekara, a harajin da zata cire a kudaden da ake buga wayar salula a hannun jama’a. Najeriya dai na daya daga cikin kasashen duniya dake da yawan masu buga waya, abin da ke kawowa kamfanoni masu zaman kansu dake samar da wayar makurdan kudaden shiga.

Gwamnati dai ta rasa wadannan kudade ne sakamakon cefanar da kamfanin waya na kasa NITEL a shekarun baya. Yanzu dai abin jira a gani shine ko ‘yan Majalisa da ita kanta gwamnati da kuma talakawa ko zasu amince da wannan shawara ta gwamnan babban bankin Najeriya.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00

XS
SM
MD
LG