Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fada Tsakanin Kabilu A Somaliya Ya Yi Sanadiyar Mutuwar Akalla Mutane 55


Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ce rikicin ya barke ne a ranar Asabar a garuruwan Abudwaq da Herale da ke yankin Galmudug kan wuraren kiwo da wuraren ruwa.

An gwabza fada ne tsakanin kabilun Dir da Marihan, wadanda suka saba yakar al-Shabaab tare shekaru da suka gabata.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ce rikicin ya barke ne a ranar Asabar a garuruwan Abudwaq da Herale da ke yankin Galmudug kan wuraren kiwo da wuraren ruwa.

Wani dattijon yankin ya shaida wa manema labarai cewa dakarun gwamnati sun isa a makare, kuma mutane 55 daga cikin bangarorin biyu sun mutu.

Wasu manyan jami’an Galmudug ba su amsa bukatar kamfanin dillancin labarai na Reuters nan take ba kan lamarin.

Ma’aikatan asibitocin da ke Herale da Abudwaq da wasu garuruwa biyu da ke makwabtaka da su sun tabbatar da cewa sun samu halartar mutane 115 da suka samu raunuka a fadan. An binne wadanda suka mutu nan take, kamar yadda mazauna garin suka ce.

Fadan dai ya lafa bayan isowar sojojin gwamnatin tarayya.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG