Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Facebook Ya Haramtawa Kamfanin Huawei Amfani Da Manhajar Sa


Kamfanin Facebook ya dakatar da damar da kamfanin wayoyin kasar China na Huawei ke da shi, na saukar da manhajar akan sababbin wayoyin kamfanin. Hakan yayi dai-dai da kokarin bin dokokin kasar Amurka da suka shafi tsaro. Kasar Amurka da China sun shiga kafar wando daya, a fagen yakin sunkuru da ya shafi harkar tsaro.

Kafin zuwa yanzu kamfanin na Huawe nada damar saukar da manhajar ta Facebook, a duk wasu sababbin wayoyin su kafin su shiga kasuwa, amma a yanzu basu da wannan 'yancin. Yau dai kamfanin ya sanar da wannan sabuwar dokar ta cewa baza su sake samun wannan damar ba.

Amma kuma an tabbatar da cewar duk wasu masu wayar ta kamfanin da suke da manhajar kamun wannan lokacin, zasu cigaba da amfani da manhajar a wayoyinsu, harma da sabunta manhajar lokaci zuwa lokaci, dokar bata shafe suba.

Amma kuma, har zuwa yanzu babu tabbaci ko mutanen da suka sayi sabuwar wayar ta Huawei, zasu iya saukar da manhajar a wayoyinsu, wannan yunkurin na kamfanin Facebook na daga cikin yunkuri na janyewar kamfanin tun bayan sa-in-sa da aka fara tsakanin kasar Amurka da China.

Tun dai a watan jiya ne ma’aikatar kasuwanci ta Amurka, ta hana kamfanonin kasar sayar da duk wasu kayan da suka shafi na’urorin zamani ga kamfanin na Huawei, harma da wasu kamfanonin kasar China baki daya.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG