Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El Rufai ya harbu da cutar coronavirus.
El Rufai ne ya bayyana hakan da kansa, a wani jawabi da ya yi wa al’umar jihar, wanda bidiyon ya karade shafukan sada zumunta.
“A farkon makon nan na kai kaina domin a yi min gwajin COVID-19, sakamakon binciken ya fito a wannan yammaci kuma ya nuna cewa ina dauke da kwayar cutar.” El Rufai ya fada a ranar Asabar.
Bidiyon jawabin da VOA ta samu mai tsawon kusan minti guda, ya nuna gwamna El Rufai a zaune sanye da doguwar riga da hula mai ruwan kofi da kuma gilashi a lokacin da yake jawabin a ofishinsa.
“Kamar yadda hukumar da ke kare yaduwar cututtuka ta NCDC ta gindaya ka’idoji ga masu dauke da cutar COVID-19 da ba su nuna alama ba, na killace kaina.”
Ya kara da cewa, “yana da matukar muhimmanci kowa ya dauki matakan kariya, a kare kai, a zauna a gida domin a tsira.”
El Rufai ya kuma jaddada cewa, “mataimakiyar gwamna, ita ce shugabar kwamitin da ke jagorantar yaki da cutar COVID-19, ni kuma zan ci gaba da fitar da sanarwa lokaci zuwa lokaci.”
Gwamna El Rufai wanda yake wa’adin mulki na biyu karkashin jam’iyyar APC, shi ne gwamna na biyu da ya kamu da cutar ta coronavirus a Najeriya.
A farkon makon nan rahotanni suka bayyana cewa gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad shi ma ya kamu da cutar.
Facebook Forum