Egypt ta gabatar da korafi a gaban hukumawa kwallon kafar Afirka ta CAF kan nada alkalin wasa dan asalin Gambia a wasan da za ta kara da Kamaru.
A ranar Alhamis din nan Egypt za ta kara da Kamaru a wasan zagayen semi-finals. Wanda ya yi nasarsa shi zai hadu da Senegal.
Sai dai hukumar kwallon kafar kasar ta Egypt ba ta bayyana dalilinta na sukar nadin alkali Bakary Gassama ba, wanda na daya daga cikin fitattun alkalan wasa a nahiyar Afirka
Dan shekaru 42, alkalin wasa Gassama shi ya hura karawar da Egypt ta sha kaye a hannun Najeriya da ci 1-0 a zagayen rukuni-rukuni a wannan gasa ta AFCON.
Har ila yau shi ne alkali da ya hura wasan da Egypt ta yi nasara da ci 2-1 akan Congo a shekarar 2017, wasan da ya ba ta damar zuwa gasar cin kofin duniya da aka yi a Rasha a 2018.
Kamfanin dillancin labaran AP ya ruwaito cewa a ranar Talata Egypt wacce ta taba lashe kofin gasar ta AFCON sau bakwai ta shigar da korafinta.
Sai dai babu wani jami’i da hukumar kwallon kafar kasar da AP ya samu zantawa da shi don jin abin da korafinsu ya kunsa.