Hukumar EFCC ta kama kudaden ne a wani shago cikin kasuwar Balogun dake tsakiyar birnin na Legas.
A sanarwar da kakakin hukumar Mr. Wilson Uwujaren ya fitar wadda ya aika wa manema labarai, ya ce wani mai kwarmatawa hukumar ne ya tona asirin inda aka boye kudin.
Kamar bayanin da ya bayar kudaden sun hada da kudin Euro 5,730 da kuma kudin Ingila pam 21,000.
A 'yan watannin baya ne gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta fitar da wani tsarin ba da tukwici ga duk wanda ya fallasa wani da ya saci kudaden gwamnati.
Tun kuma bayan haka ne, ake ta samun mutanen da ke ba da bayanan da suke kai ga gano ikudaden da ake zargin an sace ne daga aljihun gwamnati.
Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani:
Facebook Forum