Wannan shirin yiwa duk matasan kasar marasa aikin yi rajista za'a fara shi ne gobe ta kafar yanar gizo inda ake bukatar matasan su shiga yanar gizo suyi rajistan.
Kabiru Danladi Lawanti lamami a Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria yace a shekarar 2008 sun yi kokarin sanin bukatun masu daukan ma'aikata a Najeriya amma duk fannonin gwamnati da ya kamata su bada adadin wadanda suke neman aiki basu da alkalumman. Yace saboda haka wannan yunkurin na gwamnati yana da kyau.
To saidai yace hanyoyin yin rajistan ka iya zama matsala bisa ga wasu dalilai. Na daya a Najeriya ba koina ba ne ake samun yanar gizo. Na biyu ba kowa ba ne yake da kwamfuta kuma ba koina za'a sameta ba. Wasu matasan da suka koma kauye yawancinsu basu da kudin da zasu sayi wayar hannu.
Shi ma Dr. Abubakar Umar Kari na Jami'ar Abuja yace rajistan marasa aikin yi ta hanyar naura mai kwakwalwa nada matsala. Wadanda basu da aikin yi dake kauyuka da karkara sun fi na cikin birane yawa. Idan ana son shirin ya samu nasara, inji Dr Kari dole ne a samo hanyar da za'a cimma wadanda suke kauyuka da karkara a yi masu rajista amma ba lallai ta yin anfani da kwamfuta ba.
Farfasa Ibrahim Garba Sheka yace idan ana son a yi da arewa to a soma tun daga dagaci har zuwa kananan hukumomi. Shi ma Kabiru Danladi Lawanti ya kara da cewa a sanya kananan hukumomi cikin shirin.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.
Facebook Forum