Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa ta EFCC, ta ce ta fara shirin neman Birtaniya ta miko mata tsohuwar Ministar man fetur din kasar Diezani Alison-Madueke.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya na NAN, ya ruwaito cewa, kakakin hukumar ta EFCC, Mr. Tony Orilade, ya fada mata cewa, hukumar ta gabatar da wani bahasi ga sashen shari’ar kasar inda za ta nemi a mika mata tsohuwar ministar.
Ya kara da cewa, dole wannan shiri sai ya bi ta hannun ofishin babban Atoni-Janar din Najeriya, yana mai cewa ba abu ne da hukumar za ta yi gaban kanta ba.
“Nan da wasu makwanni masu zuwa, za mu bayyana halin da ake ciki kan wannan batu.” Inji Orilade, kamar yadda NAN ya ruwaito.
Madueke ta yi aiki karkashin gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.
An jima ana ta korafe-korafe kan a tiso keyar tsohuwar ministar ta mai, wacce ta tsere zuwa Birtaniya.
Ana zarginta da laifin wawure kudaden kasar a lokacin tana ofis.
A bara, wata kotun tarayya da ke Legas ta ba da umurnin a mallakawa gwamnatin tarayya Naira biliya 7.6 da aka kwace, wadanda kuma ake zargin ta sata a lokacin tana aiki.
Facebook Forum