“Mu dai muna aiki ne bisa ka’idar doka da ta kafa mu, domin yaki da cin hanci da rashawa. Kuma wasu zasu ga kamar munyi shiru a baya, wannan ya faru ne saboda lokacin gwamnonin da muke son tuhuma na da kariyar ofisoshinsu. Amma yanzu da suka kammala mulki, mun samu damar awon gaba da su”, inji jami’in labaran EFCC Wilson Owojarem akan kamawa ko garkuwa da tsofaffin gwamnoni uku da suka yi.
“Baya ga tsohon gwamnan Jigawa Sule Lamido da ‘ya’yan sa muka kama Aminu da Mustapha, mun damke tsohon gwamnan Imo Ikedi Ohakim da tsohon gwamnan Adamawa Murtala Nyako da dansa Abdulaziz, wanda dan majalisar dattawa ne mai ci. Zamu gabatar da Nyako da Ohakim gaban kotu a nan Abuja, amma Sule Lamido da muka zargi da laifukan cin hanci 27 zamu gurfanar da shi a gaban babban kotun tarayya dake Kano Alhamis dinnan” Wilson yace.
To ko hukumar EFCC tana daukar wadannan matakai ne domin burge Shugaba Muhammadu Buhari? Ohojarm yace ba haka bane. Yana mai nanata cewa doka ce ta kafa su, kuma itace suke tsare wa. Kazalika baza suyi kasa a gwiwa ba wajen magance cin hanci da rashawa.
Dama Shugaba Buhari da jam’iyyar sa ta APC sun sha nanata matukar dai aka zabe su, yaki da cin hanci zai zama kan gaba a aikin gwamnatin su.