Masana da masu fashin baki suna ganin dole ne a tashi tsaye.
Sace mutum na baya bayan nan shi ne na wani basarake da wasu suka yi a karshen makon jiya. Basaraken da aka sace kuwa shi ne wakilin tsaftar masarautar Adamawa Alhaji Aliyu Aminu Mujeli. Sai da ya kwashe kwanaki kafin a sakoshi jiya Alhamis da yamma. Lamarin ya jefa 'yanuwa da abokan arziki cikin zullumi.
Satar baya bayan nan ita ce ta karo na hudu cikin watanni hudu a jihar Adamawa. Fitattun mutane ake sacewa kodayaushe.
Misali an sace kanin tsohon shugaban hukumar EFCC Nuhu Ribadu, wato Sani Ribadu. An kuma sace kanin dan takarar gwamnan jihar a karkashin SDP Marcus Gundiri. Haka kuma aka sace dan majalisar dokokin jihar mai wakiltar mazabar Tongo.
Kakakin 'yansandan jihar DSP Usman Abubakar yace maganar sace mutane a jihar wata babbar kalubale ce domin basu saba da irn haka ba a arewa. Tunda abun yana neman ya zama ruwan dare gama gari zasu zauna su fito da tsari na musamman da zai dakile matsalar. Sun fara da wayar da kawunan jama'a kuma suna kai. Manyan mutane su dinga tafiya da masu karesu kada su fita su kadai.
Wasu suna ganin satar mutane tamkar ta zama sana'ar wasu mutane ne. Idan ba'a tashi an yi da gaske ba zata habaka ta gagari hukuma.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.