Kungiyar makiyayan ANPEN ta gudanar da wani taron a birnin Konni, inda hukumomi na bariki da na gargajiya da jami’an tsaro suka hallarta.
Inda aka yi amfani da wannan damar domin kira ga makiyaya da su taimaka domin samun zaman lafiya tsakanin su da manoma.
A jawabinsa magatakardan birnin Konni, Malam Abdu Mamedo, yace dalilin hallatar wannan taron shine domin yin godiya ga duk kungiyoyin makiyaya da Manoma, domin a wannan shekarar ba’a samu wani rikici ba wanda ya kai ga zubar da jini ba.
Wakilin sarkin Konni,Malam Ibrahim Dan Galadima, cewa yayi ya kyautu a kara hakuri da kuma kai zuciya nesa ya kara da cewa duk mai kiwon dabba kamar mai kula da karamin yaro ne.
Shugaban kunghiyar ANPEN, Malam Abdulla, yace yiwa kungiyar rajista ba shine kungiya ba aikin da takeyi shine kungiya.
Ya kara da cewa wasu shuwagabanin kungiyoyi sun maida kungiyoyin na siyasa ko kabilanci ko kuma domin neman kudi, saboda haka jama’a nada bukatar a kara wayar masu da kai saboda su gane manufar kungiya.