Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Duniya Ta Fahimci Ayyukan Ta'addancin Boko Haram a Najeriya


Hassan Muhammad, Mukaddashin Jakadan Najeriya a Amurka dake Washington DC
Hassan Muhammad, Mukaddashin Jakadan Najeriya a Amurka dake Washington DC

Jiya Muryar Amurka ta karbi bakuncin Mukaddashin Jakadan Najeriya a Amurka dake birnin Washingto DC kuma an tattauna dashi akan abubuwa da dama da suka hada da matsalar Boko Haram

Yawancin wadanda suke kai harin kunar bakin wake 'yan nan wurin ne amma an kamasu ne karfi da yaj an canza masu kwakwalwa domin su aikata duk abunda aka sasu su yi.

Inji Jakada Hassan Muhammad a yi misali da 'yan matan Chibok da suka ce su ba zasu koma wurin iyayensu ba, kuma sun yi hakan ne domin an juya musu hankali.Irin wadanan matsalolin kasashen duniya sun fahimci abun da kasar ke ciki dangane da Boko Haram

Dangane da cewa wasu na bada 'ya'yansu su yi kunar bakin wake, Jakadan yace babu wanda zai ba da 'yarsa ko dansa domin ya yi kunar bakin wake. Yana mai cewa Boko Haram sun kashe shugabannin gargajiya da masu unguwa da dai sauran shugabannin wuraren da suka mamaye da can. Wadanda suka tsira kaman a Bama da kafa suka isa Maiduguri, irinsu ba zasu ba da 'ya'yansu ba.

Akan cewa rashin Buhari ya sa aka samu karin hare hare daga Boko Haram, sai Jakadan yace ba haka ba ne. Yana ganin bayan nasarorin da suka samu sun dan huta ne shi ya sa 'yan Boko Haram suka fara afka masu.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:43 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG