Kungiyar shugabanin kananan hukumomi reshen jihar Plato ta zargi gwamnan jihar Simon Lalong da yin karan tsaye wa dokar kasa bayan ya kori dukan shugabannin kanannan hukumomin daga mukamansu.
A wani taron manema labarai da shugabannin kungiyar suka kira, sun bayyana cewa, jama’a ne suka zabe su domin haka gwamnan bashi da hurumin sauke su daga mukamansu.
Shugaban karamar hukumar Mangu, Caleb Mutfwang wanda kuma shine sakataren kungiyar shugabannin kananan hukumomin na jihar Plato ya bayyana cewa, suna kan bincike domin neman shafin da aka bashi wannan damar a kundin tsarin mulki, amma basu gani ba. Bisa ga cewarsa, gwamnatin tana yada jita-jitar cewa, shugabannin kanannan hukumomin da kansilolin da gwamnan yace ya sauke basu bashi hadin kai.
A cikin hirarsu da wakiliyarmu Zainab Babaji, wadansu daga cikin shugabannin da kansiloli da gwamnan jihar ya sauke sun bayyana cewa, zasu bi dukan matakan da doka ta ayyana wajen ganin an kiyaye kundin tsarin mulkin kasa.
A nashi bayanin, sakataren gwamnatin jihar Plateau Rufus Bature, yace matakin da gwamnatin ta dauka ya dace. Bisa ga cewarsa, gwamnan jihar ya nunawa shugabannin kanannan hukumomin cewa, gwamnati zata hada hannu da su wajen yiwa al’umma aiki, sai dai ba da dadewa ba sai gwamnatin taji sun kaita kara kotu, saboda haka gwamnatin ta yanke hukumcin sauke su bisa izinin da dokar jihar ta bata.
A cikin bayaninsa dangane da wannan lamarin, wani lauya mai zaman kansa Lewi Balakanto yace, bisa ga sashe na bakwai na kundin tsarin mulkin Najeriya, gwamna bashi da hurumin sauke shugabannin kanannan hukumomin da al’umma suka zaba. Bisa ga cewarshi, kotun kolin kasar ta yanke hukumci cewa, idan zabe aka yii, babu wanda yake da izinin cire mutum sai wadanda suka zabe shi.
Ga cikakken rahoton.