Sama da masu gudu dubu 50 da ‘yan kallon da aka yi kiyasin za su kai miliyan daya ne za su halarci gasar, yayin da masu gudun za su ratsa hanyoyin da aka shata masu wadanda za su bi ta unguwannain Staten Island da Brooklyn, da Queens da Bronx da kuma Manhattan a gudun da za su yi na tsawon mil 26.2.
Tun dai da aka kirkiro wannan gasar a shekarar alif- dari-tara-da-sabi’in (1970), ba a taba samun mace da ta lashe gasar ba, amma akwai alamu Buzunesh Deba na da damar samun nasara a wannan karo.
Domin tarihi ya nuna cewa Deba ita ce tafi kowace mace iya gudu a Birnin New York, in da ta taba lashe gudun fanfalakin da aka yi a Boston a shekarar 2014 cikin sa’oi biyu da mintina 19 da dakikoki 59, nasarar da ta bata damar kafa tarihi.
Facebook Forum