A wani taron manema labarai kwamishanan 'yansandan jihar Neja Alhaji Abubakar Marafa yace sun dauki matakin ne domin tabbatar da an gudanar da bukukuwan cikin kwanciyar hankali.
Alhaji Abubakar Marafa yace yana anfani da damar taro da manema labarai ya tabbatarwa kiristoci maza da mata cewa zasu kiyaye da lafiyarsu da dukiyoyinsu lokacin bukukuwan. Ta dalilin haka kimanin 'yansanda dubu biyar zasu bazu a duk mijami'u da duk inda jama'a ke taruwa domin su tsare rayuwarsu da kayansu.
Banda zuwa mijami'u 'yansandan zasu je kasuwanni da otel otel da duk inda jama'a zasu taru. Kazalika zasu kara yin sintiri zuwa kowane sako.
Shugabannin kiristoci sun ce sun gamsu da irin matakan da jami'an tsaron ke dauka. Amma shugaban kungiyar kiristocin jihar Neja Rabaran Musa Dada yace a wannan kirsimatin zasu gudanar da addu'o'i na musamman domin tunawa da wadanda suka rasa rayukansu a harin da aka kai a mijami'ar St. Theresa dake garin Madalla a shekarar 2012.
Saidai bukukuwan na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da matsanancin karancin man fetur lamarin da ya jefa jama'a cikin wani yanayi na takura.
Ga karin bayani.