SOKOTO, NIGERIA - Marasa lafiya fiye da dubu daya suka samu kulawa da samun magani kyauta, yayin da fiye da dari daya aka yi musu tiyata a Jihar Sakkwato dake arewa maso yammacin Najeriya.
Yanayin da jama'a suke ciki a Najeriya na fatara da yanayin tsadar rayuwa na daga cikin abubuwan da ke sa marasa lafiya masu karamin karfi zama da ciwo na tsawon lokaci saboda ba su da sukunin neman waraka a asibitoci.
Yusha’u Abdullahi daga Jihar Zamfara daya daga cikin marasa lafiya maras galihu ya ce yana fama da rashin lafiya a kodarsa tsawon shekaru uku, kuma ya yi ta zama a asibitin Gusau kafin ya koma Sakkwato yana fama da matsalar ne saboda rashin karfin daukar nauyin yi masa tiyata.
Yusha'u Abdullahi na daga cikin marasa lafiya da suka yi sa'ar shiga cikin wadanda likitocin da ke yawo kasashen duniya don bayar da tallafin kiwon lafiya suka shata yi wa aikin tiyata, kuma tuni sun yi wa wasu aiki cikin nasara.
Aisha Abdullahi na daga cikin wadanda aka yi wa tiyata saboda ciwon makoko da ya fito mata, ita ma kuma an yi aikin cikin nasara.
Wannan shi ne karo na biyu da lokitocin suka gudanar da aikin bayar da tallafin kiyon lafiya kyauta a Sakkwato, baya ga wasu jihohi da suka saba ziyarta a Najeriya.
Dokta Arfan Ali shi ne jami'in da ke kula da aikace-aikace na likitocin, “ya ce sun hada ayarin likitoci 25 daga kasashen Ingila, Saudi Arabia, Jordan da kasashe da yawa suka isa Sakkwato, suna zagayawa kauyuka da wurare daban-daban suna bayar da tallafin kula da lafiya kyauta har ma da yin tiyata ga masu bukatar hakan, suna da wani ayari a asibitin da ake kula da mata masu yoyon fitsari, kai muna gudanar da ayyuka har nau'i uku zuwa hudu”.
Hukumar zakka da wakafi ta Jihar Sakkwato ita ce tayi ruwa tayi tsaki ga zuwan likitocin Sakkwato a shekarar bara da wannan kuma shekara.
Muhammad Lawal Maidoki shugaban hukumar ya ce suna yi ne saboda saka farin ciki da kuma taimakon marasa lafiya mabukata wadanda ke fama da ciwo shekara da shekaru ba su da mai yi musu, kuma da ma aikin da hukumar Zakka ke yi na tsawon lokaci.
Yace saboda dadin da likitocin ke ji idan sun zo Sakkwato yanzu har an samar musu ofishi wanda zai zama ofishinsu na Najeriya.
Kungiyar likitoci Musulmi ta Najeriya reshen Jihar Sakkwato wadda ke aiki tare da ayarin likitocin da suka zo, ta ce kowannensu na amfana da juna.
Dokta Muhammad Shu'aibu Gobir shugaban kungiyar likitocin ya ce ayarin likitocin da suka yi aiki tare a asibitin Maryam Abacha sun koyi kwarewar da ke ga likitocin gida, har ma sun gayyaci wasu daga cikinsu suka je kasar Somaliya suka gudanar da irin wannan aiki na taimakon jama'a na tsawon kwana takwas, wanda a kwanannan ne suka dawo.
Saurari cikakken rahoton daga Muhammad Nasir: