Dubban jama’a a birnin Lorca na kudancin kasar Spain sun kwana a waje saboda suna fargabar karin girgizar kasa bayan wasu tagwayen girgizar kasar da aka yi suka haddasa hasarar rayuka jiya laraba. Jami’ai a yankin Murcia mai farin jinni ga ‘yan yawon bude ido, sun fada yau Alhamis cewa akalla mutane takwas ne girigizar kasar ta kashe, ta rushe gidaje da majami’u da kuma wasu wurare na tarihi. Ba kamar yadda rahotanni daga farko suka bayyana cewa mutane 10 ne suka halaka, yanzu an tabbatar cewa mutane takwas ne su mutu.
Masu aikin agaji sun raba borguna da kayayyakin abinci da kuma ruwa ga mazauna garin Lorca, yayinda ko ina ka duba sai kaga rusassun gine gine da motoci da suka lallace birjit gani a tituna.