WASHINGTON, DC —
Yau shirin Domin Iyali ya samu yin hira da wata matashiya ‘yar shekaru 17 da zamu saya sunanta, wadda ta kashe wata ‘yar shekaru 28 a Kano bayan sun sami sabani. A cikin hirar shirin da kwararru, sun bayyana matsalolin da ke sa matasa daukar doka a hannunsu.
Wakiliyarmu Baraka Bashir ta yi nazarin wannan lamarin. Saurari rahoto na musamman da ta hada mana:
-
Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.