A shekara ta 2003, Najeriya ta amince da dokar kare hakkin kananan yara don jihohi su amfani da ita bayan yi mata kwaskwarima yadda za tafi daidai da al’adu da kuma addinansu. Dokar kare hakkin yara ta 2003 ta fadada yancin dan adam da aka baiwa yan kasa a cikin kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ga yara. Duk da cewa an zartar da wannan doka a matakin tarayya, amma zata yi aiki ne kawai idan majalisun jihohi su ma sun rungume ta sun maida ita doka.
A yau shirin Domin Iyali zai fara nazarin tasirin wannan doka ko akasin haka shekaru sama da 20 bayan amincewa da ita a Najeriya, batun da aka gabatar aka kuma yi muhawara a kai a babban taron kungiyar lauyoyi mata na kasa da aka gudanar a birnin Kano.
Saurari cikakken shirin:
Dandalin Mu Tattauna