A ci gaba da nazarin hanyar shawo kan yawan mace macen aure a Jamhuriyar Nijar, yau shirin zai dora a inda Malan sani Sabiou Souleyman shugaban kungiyar addinin Islama ta Aisef ya ke bayani kan yadda saba koyarwar addini ke taka rawa a mace macen aure.
Saurari tattaunawar da wakilin Sashen Hausa Souley Moumouni Barma ya jagotanta da ta hada kan masu ruwa da tsaki da suka hada da Hajiya Halima Sarmay dattijiya kuma daya daga cikin shugabannin kungiyar kare hakkin mata da kananan yara da kuma Falmata Moctar Taya shugaban kungiyar matasa: