WASHINGTON, DC —
A wannan shirin, mun hada kan masu ruwa da tsaki domin neman sanin masababin yawan mace macen aure da ake fuskanta a Jamhuriyar Nijar,da nufin neman hanyar maganceta.
Bakin da muka gayyata su ne,Hajiya Halima Sarmay dattijiya kuma daya daga cikin shugabannin kungiyar kare hakkin mata da kananan yara, da Malan Sani Sabiou Souleyman shugaban kungiyar addinn Islama ta Aisef, da kuma Falmata Moctar Taya shugabar kungiyar matasa.
Wakilinmu a birnin Yamai Souley Moumouni Barma, ya fara da tambayar Hajiya Halima Sarmay, yadda suke ganin wannan rahoton da kuma abinda suke ganin ya haddasa wannan matsala.
Saurari bayaninta da kuma karin bayanai daga sauran bakin da muka gayyata: