A yau shirin Domin Iyali ya gayyaci matasa domin tofa albarkacin bakinsu a yunkurin da ake yi na shawo kan matsalar fyade da ta buwayi al’umma a Najeriya, abinda ya sa mata gudanar da zanga zanga a birane da dama na kasar.
Wannan lamarin ya sa aka kakkafa kungiyoyin fafatuka da tada tsimin al’umma a matakai daban daban.
Matasan da wakiliyarmu Baraka Bashir ta tattauna da sun sune Zainab Nasir Ahmed, Salim Wada Usman, Ibrahim Bala, Safiya Daba, Zilahayuwas Danjuma.
Saurari shirin domin jin kungiyoyin da suke wakilta da kuma yadda suke kallon lamarin.
-
Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.