A ci gaba da nazarin matakan shawo kan matsalar fyade da ke ci gaba da karuwa a Najeriya, yau zamu duba hukumcin da ya kamata a yankewa masu aikata wannan laifin.
Wadanda muka gayyato domin tattaunawa kan batun sun hada da kwamishinar ma’aikatar harkokin mata ta jihar Nassarawa Halima jabiru, da Saudatu Mahdi shugabar kungiyar kare hakkokin mata da kananan yara WRAPA, da Safiya Adamu, daya daga cikin shugabannin kungiyar dake hankoron kare hakkokin kananan yara da ake kira Tallafi Najeriya, sai kuma Aisha Buba kwararriya a fannin sanin halayyar dan adam.
A wannan shirin, Jagorar wannan tattaunawa, Shamshiya Hamza ta fara da tambayar kwamishinar ma’aikatar harkokin mata ta jihar Nassarawa Halima Jabiru hukumcin da ake yiwa wadanda aka samu da wannan laifin.
Saurari cikakken shirin
Facebook Forum