Idan kuna biye da mu, shirin domin iyali ya karbi bakuncin Madam Eneh Ede ‘yar fafatukar kare hakkokin mata, kuma wadda ta taba tsayawa takara a matsayin mataimakiyar gwamna a jihar Binuwe, da ‘yar gwaggwarmaya Barrister Hassana Ayuba Mairiga, da kuma dan siyasa a jihar Kano Nasir Shuaibu Marmara, wadanda su ke nazarin kalubalen da ke gaban mata a cimma burinsu na samun kaso 35 cikin dari na guraban siyasa a Najeriya .
Saurari ci gaban tattaunawar da Medina Dauda ta jagoranta:
-
Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.