A ci gaba da zanarin kalubalen da ke gaban mata a yunkurin cimma burinsu na samun kaso 35 cikin dari na guraban siyasa a Najeriya, da nufin neman mafita, a makon da ya gabata, Madam Eneh Ede ta fara bayani kan kalubalen da mata ke fuskanta a fagen siyasa lokaci ya kwace mana, inda kuma za mu tashi ke nan yau a tattaunawar da wakiliyarmu Medina Dauda ta jagoranta.
Saurari cikakken shirin:
-
Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.