A shekarar dubu da dari biyu da goma sha biyar, Najeriya ta zartar da dokar haramta cin zarafin mutane da ake kira (VAPP), ciki har da cin zarafin mata, cin zarafi a cikin gida, da kuma haramta bin al'adun gargajiya masu cutarwa. Dokar ta kuma bukaci bada kariya ta doka da ma'amala da tallafa wa wadanda abin ya shafa, da kuma hukunta masu laifi. Sai dai bayan kusan shekaru goma da kafa wannan doka a matsayin tarayya, har yanzu batun yana kasa yana dabo a galibin jihohin kasar.
Batun da Shirin Domin Iyali ya fara haska fitila a kai ke nan yau tare da Hajiya Hauwa Abubakar Funtua mai ba matar gwamnan jihar Katsina shawarwarwari, da ‘yar gwaggwarmaya Jamila Sidi Ali Sirajo, da kuma Barrister Hassana Ayuba Mairiga Tula.
Saurari cikakken shirihn:
Dandalin Mu Tattauna