Tun da aka fuskanci karuwar fyade a Najeriya, kungiyoyin kare hakkin bil'ama da kuma daidaitun jama'a suka shawarta sake salo da kuma hukumci mai tsanani da zai zama ishara ga masu aikata wannan cin zarafin, kama daga hukumcin kisa zuwa dandaka.
To gwamnatin jihar Kaduna ta shiga gaba a daukar wannan matakin inda ta kafa dokar dandake wanda aka samu da wannan laifin. Abinda shirin Domin Iyali ya nazarta ke nan a yau.
A cikin hirarsu da wakilinmu Isa Lawal Ikara. Kwamishinar ma'aikatar harkokin mata ta jihar Hajiya Hafsat Mohammed Baba, ta bayyana yadda suke kallon wannan doka da ta ce sun yi na'am da ita, ta kuma ce zasu bi ta sau da kafa domin ganin an yi wa wadanda ake zalunta adalci.
A nashi bayanin lauya mai zaman kansa, kuma mai bibiya kan lamura, El-Zibairu Abubakar ya bayyana matsalolin da yake gani zasu iya kadangaren bakin tulu dangane da wannan yunkuri .
Saurari cikakken shirin:
Facebook Forum