Duk gidajen man da ke tsakiyar birnin na cike da motoci inda masu sayar da man a jarka ke sayarwa kan farashi mai tsadar gaske.
Baya ga bayanan da a ka samu a kwanakin baya daga shugaban kamfanin fetur NNPC Mele Kolo Kyari cewa akwai wadataccen man, ba wani bayani na dalilin wannan karancin man.
Akwai ma rade-radin da ke nuna wasu gidajen man sun kara farsahin litar mai biyo bayan batun kara farashin man ta bayan gida.
Gidan man da Muryar Amurka ta ziyarta a AREA 3 na da dogon layi amma bai kara farashin ba da ya wuce sauyawa daga Naira 162 zuwa 165.
Tun janye batun karin farashin litar fetur a farkon watan nan a ke ta samun cikas wajen wadatar man, kazalika an samu matsalar kawo mai mai illa da ya haddasa samun matsala ga motoci.
Kamfanin NNPC ya bayyana cewa man na dauke da wani sinadari ne na “methanol” da ya wuce kimar da Najeriya ke amfani da shi.