Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Oando Na Najeriya Ya Musanta Shigo Da Gurbataciyar Man Fetur


Oando
Oando

Kamfanin mai na Oando na Najeriya yace bai shigo da man fetur marar inganci ba a cikin kasar, kamar yadda ake zargi.

Kasar da ke yammacin Afirka na fuskantar karancin mai bayan isar da iskar gas mai dauke da sinadarin methanol mai yawa. Najeriya dai ta dogara ne gaba daya kan shigo da kaya daga kasashen waje domin biyan bukatunta na man fetur a cikin gida.

Kamfanin mai na Oando, ya ce ta samar da man fetur wanda ya dace da ka'idojin shigo da mai ta Najeriya.

Rubutacciyar sanar da kamfanin ya fitar ta kara da cewa,“Bayan rahotannin da kafafen yada labarai suka bayar da Oando a matsayin daya daga cikin hudu na masu shigo da kaya da suka samar da iskar gas mai hade da sinadarin methanol (PMS) zuwa cikin kasar nan, muna so mu bayyana cewa Oando ba ta shigo da kayan PMS wanda ya lalace ko mara inganci ba."

A ranar alhamis din da ta gabata ne shugaban kamfanin mai na kasa NNPC, Mele Kyari, ya ce an shigo da gurbataccen man fetur mai sinadarin Methanol da ya wuce kima daga kasar Belgium ba tare da an gano shi ba da kuma kamfanonin da suka shigo da shi a karshen watan Janairu.

Kyari ya ce kamfanoni hudu ne suka shigo da man fetur din - MRS Oil Nigeria, Emadeb/Hyde/AY Maikifi/Brittania-U consortium, Oando da kuma Duke Oil wanda daya daga cikin kananan kamfanonin da ke karkashin NNPC.

Kamin mai na Oando ya ce, ya himmatu wajen hada kai da kamfanin NNPC da kuma masana’antu domin gano musabbabin gurbatar man.

‘Yan majalisar dokokin Najeriya sun gabatar da kudirin neman kamfanin mai na kasa NNPC ya dakatar da kuma gudanar da bincike kan kamfanoni hudu yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin a tuhumi dukkan wadanda aka samu da laifi.

NNPC ya ce kasar ba ta gano wani sinadarin methanol fiye da yadda aka saba a shigo da mai a baya-bayan nan ba saboda a aikin tantance ingancin man fetur din babu batun tantance kaso na sinadarin Methanol a ciki.

- REUTERS

XS
SM
MD
LG