Kimanin mutane sama da kashi hamsin da shidda da ga cikin dari su ka fita runfunan zabe a ranar Laraba domin kada kuri’a a zaben yan majalisar wakilai, cikin shekaru goma, a yankunan Jammu da Kashmir, yankin da ake takaddama a kai da ke karkashin ikon Indiya.
'Yan takara 239 ne suka fafata a mazabu 26 na kujerar yan majalisu a Ranar Laraba, a kashi na biyu na zagaye 3 na zaben. Mutanen da suka cancanci kada kuri’a su sama da miliyan biyu ne da dubu dari biyar. An dai gudanar da zaben bisa tsauraran matakan tsaro, domin tabbatar da ganin komi ya gudana lami lafiya.
Babban jami’in zabe a yankin Pandurang Kondbarao Pole, ya shaidawa manema labarai cewa, an gudanar da zabe lami lafiya a daukakin gundumomin shidda, sai dai, duk da haka yace, akwai dan abin da ba za a rasa ba kamar yar gardama nan da can da aka samu a wasu wurare, wanda hakan ba ya bukatar a sake kada kuri’a.
Wannan shine karon farko da al’ummar yankin Jammu da Kashmir ke gudanar da zabe tun bayan da gwamnatin Firai Minista Narendra Modi da jam’iyyar sa mai mulki ta Bharatiya ta soke takaitaccen ikon ta a shekarar 2019.
Wasu mazauna yankunan sun yi ma zaben kallon tamkar wani yaki tsakanin BJP da mutanen Kashmir, da su ka ce, gwamnati ta kwace musu hakkokinsu a gwamman shekaru.
Wani mazaunin Qamarwari da ke yankin, Ikhlaq Shah, ya shaidawa Muryar Amurka cewa, '‘duk da lokacin da aka dauka ana kiraye-kirayen daukar matakan da su ka dace, nayi watsi da yin zabe tun bayan da shekaruna su ka kai na inyin zaben.
''To amma a yau ina jin ya zama wajibi in kada kuri’a ta kuma in aika sako zuwa New Delhi. Idan har mu ka kuskure ba mu yi wani abu ba a yanzu, nayi Imani gwamnatin BJP za ta kakaba mana abinda ta shirya yi a kan mu”.
Ya kuma zargi Indiya da bukatar rika tatsar albarkatun kasar Jammu da Kashmir, amma ba kula da mutanensu ba.
Wani mai sharhi kan al’amurran siyasa Muzamil Maqbool, ya shaidawa Muryar Amurka cewa, jam’iyyun siyasa sun yi rauni matuka saboda shugabanni sun fi fifita son zuciyar su.
Dandalin Mu Tattauna