Shugabannin kasashen duniyar da aka zaba don su taimaki Ivory Coast wajen murmurewa daga wata da watannin da ta yi cikin tashin hankali sun gana da sabon shugaba da kuma shi wanda ya hambare kwanan nan.
Mambobin wannan kwamitin, wadanda ake kira dattawa, sun gana jiya Litini da tsohon shugaba Laurent Gbagbo a birnin Korhogo da ke arewacin kasar, inda aka masa daurin talala.
Bayan ganawar, Archbishop Desmond Tutu na Afirka ta Kudu ya ce Mr. Gbagbo ya bayyana burin ganin Ivory Coast ta koma kamar da. Tutu y ace ya yi farin ciki da kalaman na Mr. Gbagbo.
Tawagar ta hada das hi Tutu, tsohon Sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya Kofi Anan da tsohuwar shugabar Irland Mary Robinson.
Tawagar ta gana da Shugaba Alassane Ouattara jiya Lahadi a birnin Abidjan.
Mr. Ouattara ya nemi da a dawo da harkoki kamar yadda su ke a da a Ivory Coast kuma ya sha alwashin kafa kwamitin tsage gaskiya da kuma sulhu.