Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Dake Biyayya Ga Alassane Ouattara Sun Kai Hari Kan 'Yan Banga

'Mayakan sakai dake biyayya ga Ibrahim Coulibaly suke sintiri a unguwar Abobo,dake Abidjan.
'Mayakan sakai dake biyayya ga Ibrahim Coulibaly suke sintiri a unguwar Abobo,dake Abidjan.

Mayakan sa kan dake goyon bayan sabon shugaban kasar Ivory Coast Alassane Ouattara,sun sake kai wasu hare hare kan ‘yan bangar da suka taimaka wajen hambaras da tsohon shugaba Laurent Gbagbo.

Mayakan sa kan dake goyon bayan sabon shugaban kasar Ivory Coast Alassane Ouattara,sun sake kai wasu hare hare kan ‘yan bangar da suka taimaka wajen hambaras da tsohon shugaba Laurent Gbagbo.

Shaidun gani da ido sun tabbatar da rahoton cewa sun ga mayakan dake marawa Alassane Ouattara sun kai hari kan shugaban ‘yan banga Ibrahim Coulibaly laraban nan, a dabarsa dake unguwannin Abobo, birnin Abidjan, bayan kuwa a lokacin da ake fafitikar korar Laurent Gbagbo,‘yan bangar ne ke taimaka masa.

A halin da ake ciki, sabuwar Gwamnatin kasar Ivory Coast tace ta kafa wata hukumar bincike da zata fara gudanar da bincike kan katobarar da tsohon shugaba Laurent Gbagbo ya aikata, hart a kaia saida aka kai ga kamashi aka tsare saboda yin watsin da yayi da sakamakon zaben da aka gudanar cikin ‘yanci da walwala a Ivory Coast.

Mai Magana da yawun Gwamnatin Ivory Coast Patrick Achi, yace tsohon shugaban na Ivory Coast ya aikata manyan laifukan da za’a tuhumeshi tare da uwargidansa da manyan masu mara masa baya, amma yaki bayyana manyan laifukan da za’a tuhumi Laurent Gbagbo.

XS
SM
MD
LG