Haka kuma ta bangaren Nijar wasu tankoki sama da 100 ke can girke a garin Tera na jihar Tilabery dauke da mai akan hanyarsu ta zuwa Burkina Faso da Mali ke jiran samun rakiyar jami’an tsaro yau kwanaki a kalla 10 abin da ya sa kungiyar drebobi da ‘yan kasuwa suka fara kiraye kirayen ganin mahukunta sun dauki mataki.
Yawaitar ayyukan ‘yan ta’adda akan hanyar da ke hada garuruwan Cinkasse da Bitou da Fada da Kantchari ta bangaren Burkina Faso zuwa garin Torodi dake Nijar ya sa matafiya ke dogon kewaye domin bi ta garin Dori da nufin samun rakiyar jami’an tsaro to sai dai a wannan karon samun rakiyar ya faskara. lamarin da ya rutsa da trelolin Nijar kimanin 300 akan iyakar Burkina Faso bayan fitowarsu daga Ghana da Togo dauke da lodi.
Gamatche Mahamadou na daga cikin shugabannin kungiyar drebobi ta kasa. Ya kuma ce direbobin mazauna Nijar suna cikin wahala saboda maimakon su yi tafiyan sati daya ko biyu, sai su yi kusan wata daya kan hanya, don haka dole kaya su yi tsada.
Makwanni kusan 2 kenan da wadanan motoci ke jibge cikin halin jira yayinda ta bangaren Nijer ma wasu motocin dakon may a kalla 180 ke garin Tera na Jihar Tilabery dauke da lodin da ya kamata su sauke a Burkina Faso da Mali amma kuma su din ma rashin samun rakiya ya hana masu tsallaka iyaka.
Kawo yanzu ba wani bayani a hukunce daga bangaren Nijar ko Bukina Faso dangane da dalilan dakatar da tsarin raka matafiya don haka kungiyar drebobi, a ta bakin sakatarenta, ke ganin bukatar tsoma bakin shugaban kasar Nijar don warware wannan kulli.
Sakataren kungiyar ‘yan kasuwar Nijar dake shigo da kaya daga waje Chaibou Tchombiano da na tuntuba a kan wannan batu ya bayyana min cewa ya na ci gaba da tattara bayanai domin tantance zahirin girman matsalar da abin ya haddasa.
Matsalar tsaro a yankin sahel sakamakon mamayar da ‘yan ta’adda suka yi wa kusan kashi 40 na fadin kasar Burkina faso, kamar yadda arewacin Mali ma ke hannun mayakan jihadi, abu ne da ya shafi garuruwa da dama na iyakar Nijar da wadannan kasashe lamarin da sannu a hankali ke shafar sha’anin zirga zirgar jama’a , a baya an kiyasta gwamman motocin dakon albasa da na man fetur da na iccen girki da ‘yan ta’adda suka kona kurmus, mafari kenan da matafiya ke dari darin kama hanya ba tare da rakiyar dakarun gwamnati ba.
Saurari rahoton Sule Barma: